15 Janairu 2022 - 19:25
​Guinea: An Kaddamar Da Bincike Kan Tsohon Shugaba Alpha Conde

Gwamnatin mulkin sojin kasar Guinea, ta kaddamar da binciken shara’a, kan zarge-zargen cin zarafin bil’adama da ake yi wa hambararren shugaban kasar Alpha Conde.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Babban lauyan gwamnati a kotun daukaka karar Guinea Alphonse Charles Wright ne ya ba da umarnin gudanar da bincike kan "mahimman bayanai dangane da laifukan ake zargin wasu mutane da aikatawa a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2020, wadanda har yanzu ba a bayyana sunayensu ba.

Alpha Conde dai ya kasance shugaban kasar Guinea daga 2010-2021 kafin sojoji su yi masa juyin mulki a watan Satumban da ya gabata karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumbouya, shugaban gwamnatin soji mai ci a yanzu.

Sanarwar kaddamar da bincike kan laifukan da aka tafka a karkashin gwamnatin da ta gabata, ta zo ne bayan da a karashen shekarar da ta gabata, aka baiwa tsohon shugaba Conde, izinin tafiya kasar waje tsawon wata guda domin neman lafiya, wanda a yanzu yake tsare a karkashin daurin talala a gidansa da ke birnin Conakry.

Sakin Conde mai shekaru 83 dai na daya daga cikin bukatun kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta gabatarwa sojojin Guinea, baya ga gudanar da zabe cikin watanni shida.

Kungiyar ta ECOWAS ta dakatar da kasar Guinea daga cikinta tare da sanyawa wasu ‘yan majalisar mulkin soji takunkumin da suka nada Kanal Mamady Doumbouya a matsayin shugaban rikon kwarya na kasar mai arzikin ma’adinai.

342/